Zoetrope na Amurka

American Zoetrope (wanda aka fi sani da Omni Zoetrope an kafashi daga shakara ta 1977 zuwa 1980 da Zoetrope Studios daga 1980 har zuwa 1990) kamfani ne mai zaman kansa na samar da fina-finai na Amurka, wanda aka kafashi a garin San Francisco, California kuma Francis Ford Coppola da George Lucas ne suka kafa shi.

An buɗe shi a ranar 12 ga watan Disamba shekara ta1969, [1] kanfanin ba samar da fina-finai kawai yake ba ya samar da su Apocalypse Now, Bram Stoker's Dracula da Tetro, har ma da fim din George Lucas kafin Star Wars THX 1138, da kuma wasu da yawa daga daraktocin avant-garde kamar Jean-Luc Godard, Akira Kurosawa, Wim Wenders da Godfrey Reggio. American Zoetrope ya kasance farkon mai karɓar fim na dijital, gami da wasu daga cikin farkon amfani da HDTV.[2]

Fim hudu da American Zoetrope ta samar an haɗa su a cikin Fim 100 na Cibiyar Fim ta Amurka. Fim din da aka samar da Zoetrope na Amurka sun sami lambar yabo ta Kwalejin 15 da kuma gabatarwa 68.

American Zoetrope yana cikin Ginin Sentinel
  1. Fog City Mavericks. Starz, Englewood, CO, USA. June 15, 2011. Television.
  2. "Francis Ford Coppola". UCLA School of TFT. Archived from the original on 2023-06-13. Retrieved 2023-06-13.

Developed by StudentB